Sojoji sun kashe dan ta’adda Ali Kachalla da kwamandojin Dogo Gide
Jiragen sojin Najeriya sun kashe dan bindiga Ali Alhaji Alheri, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau da kuma yaran Dogo Gide
Sojojin sama na Najeriya sun kashe kasurgumin dan bindiga, Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Jihar Zamfara.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, cewa an kashe Kachalla Kawaje ne ranar Litinin a Jihar Neja.
- Gwamnatin Borno na raba wa ’yan gudun hijira dabbobi 5,000
- Osimhen da Asisat Oshiola sun zama gwarazan ’yan wasan Afirka na 2023
Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 6 ga watan na Disamba, jiragen soji suka kai hari sansanin Ali Kachalla da Dogo Gide, suka kashe wasu gaggan ’yan ta’adda.
Wadanda aka kashe sun hada da Machika (kanin Dogo Gide, kwamanda a kungiyar Gide) da Dan Muhammadu, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin Dogo Gide.
Kasurguman ’yan bindigan uku tare da wasu da dama, an kashe su ne a lokacin da suke kokarin kai hari a Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa Dogo Gide da Ali Kachalla sun addabi sassan jihohin Zamfara da Neja.