Sojoji sun kashe jagoran Boko Haram Abu Shekau a Yobe

Dakarun sun daƙile harin tare da hallaka jagoran Boko Haram, Abu Shekau.

Sojoji sun kashe jagoran Boko Haram Abu Shekau a Yobe

Dakarun Rundunar Operation Haɗin Kai tare da haɗin gwiwar ’Yan Banga, sun yi nasarar daƙile harin da Boko Haram suka kai unguwar Sabon Fegi da ke Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Wasu majiyoyin leƙen asiri, sun shaida wa Zagazola Makama cewa, maharan sun kai harin da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Alhamis.

Harin ya yi sanadin mutuwar mahara huɗu ciki har da wani Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Shekau.

Wani mazaunin garin Yadin Buni da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewar dakarun soji sun taka rawar gani wajen ragargazar ‘yan ta’addan.

Dakarun sojin sun yi nasarar daƙile harin ta hanyar hana mayaƙan Boko Haram shiga yankin.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan, lamarin da ya tilastawa wasu tserewa.

Abu Shekau, wanda yake mai ra’ayi irin na tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ana ɗaukarsa a matsayin babban jigo a cikin ƙungiyar.

Abu Shekau, ya sanya wa ɗansa sunan Abubakar Shekau a matsayin girmamawa ga tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram.