Sojoji sun kashe jagoran ISWAP, Abu Jirir a Yobe

Kisan Abu Jarir ya kawo babban koma-baya ga tsarin shugabancin ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Sojoji sun kashe jagoran ISWAP, Abu Jirir a Yobe

Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe wani fitaccen ɗan Majalisar Shura ta ƙungiyar ’yan ta’addan ISWAP a wani samame da suka kai a Jihar Yobe.

Majiyoyin tsaro sun ce an tabbatar da wannan lamari da misalin qarfe 6:12 na yamma a ranar 22 ga Afrilu bayan rahotannin leƙen asiri da ke cewa sojoji sun kashe babban ɗan ta’addan, wanda aka bayyana da Abu Jarir, a yankin Babbangida cikin Ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

A cewar majiyoyin sojan, kisan Abu Jarir ya kawo babban koma-baya ga tsarin shugabancin ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa babban kwamandan ISWAP a yankin tafkin Chadi, wanda aka bayyana da Ba Shuwa, ya tura wata tawaga don gano gawar Abu Jarir a ranar da abin ya faru.

An ce an ga tawagar bincike tana gurgusowa a kan babura kusan 12 na rana a kusa da yankin Aljanna Jaule.

Ana sa ran karin bayani kan wannan aiki yayin da ake ci gaba da cin binciken lamarin.