An kashe shugaban masana’antar bom na kungiyar ISWAP

Muhammadu ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake jagorantar wani taron hada ababen fashewa na ISWAP

An kashe shugaban masana’antar bom na kungiyar ISWAP

Sojojin rundunar Operation Desert Sanity II sun kashe kwamandan masana’antar kera ababen fashewa na kungiyar ISWAP, Malam Muhammad, a Dajin Sambisa.

Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun aika Muhammadu lahira ne a wani kazamin gumurzu a ranar 14 ga watan Mayu a sansanin ’yan ta’addan a Ukuba da Njimia a Karamar Hukumar Bama.

Kamar yadda zagazola makama masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi ke cewa, Malam Muhammadu ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya jagoranci wani taron bitar ISWAP kan kirkire-kirkiren abubuwan fashewa.

Suna cikin taron ne sojoji suka rutsa shi da mayakan kungiyar ne suka aika su lahira.

Muhammadu ya sha aika kananan yara su kai harin kunar bakin wake ta hanyar tayar da bama-bamai, ciki har da ’ya’yansa uku.

Wasu majiyoyin leken asiri sun kara  shaida wa Zagazola Makama cewa sojojin sun kuma kama wata mota dauke da bama-baman da aka kera domin kai wa sojoji hari da ita.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos