Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga a Kaduna
Janari da wasu ‘yan bindiga ne suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Dakarun rundunar sojin “Operation Whirl Punch” ta kashe wani kasurgumin dan bindiga mai suna ′Janari′ a Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet ne, ya bayyana hakan a Abuja ranar Lahadi.
- An sako mutanen da aka sace a rukunin gidaje a Abuja
- An yi canjaras tsakanin Algeria da Burkina Faso a Gasar AFCON
Ya ce, Janari da wasu mukarabbansa sun jima suna sace mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce an bayar da izinin kai samamen ne, bayan da aka hangi Janari da wasu ‘yan bindiga a wani waje kusa da Gadar Katako a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Gabkwet, ya kara da cewa bayanan sirri sun nuna cewa ’yan bindigar na shirin kai hari ne lokacin da aka kai musu samame.
“Rahoton sirri da aka samu sun nuna cewa an kashe Janari tare da wasu ‘yan ta’adda a yayin harin.
“An kuma kai harin ne ta sama a ranar Asabar kan maboyar ‘yan ta’addan a kusa da garin Chukuba da ke Jihar Neja.
“Bayan harin an samu rahotanni da suka nuna an kawar da abun harin da ake nema.
“Za a ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin sojin sama da sauran hukumomin tsaro don kawar da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane,” in ji Gabkwet.
A baya-bayan nan dai ‘yan bindiga sun matsawa hanyar Kaduna zuwa Abuja da hare-hare, inda suka sace mutane da dama.