Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Abu Nasr ne ya jagoranci kai hari garin Rann a makon da ya gabata.

Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno.

A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann.

Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi.

Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196.

Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa Rann daga Kamaru, ya mutu tare da wasu ’yan ta’addan.

An kuma samu nasarar ƙwato bindigogi, harsasai, bama-baman roka da sauran abubuwan fashewa.

Harin ya faru daga ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, zuwa safiyar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025, tare da taimakon bayan jiragen sojojin sama.

A cewar jami’an tsaro, an gano gawarwakin ’yan ta’adda bakwai a wajen, kuma akwai yiwuwar sama da hakan sun rasu.