Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300
Rundunar sojojin Operation FANSAN YAMMA ta ce, sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ’yan bindiga mai suna Alhaji Tukur a Zamfara, tare da daƙile hare-hare a Zamfara da Katsina. Rundunar ta kuma ce samamen jiragen yaƙin sojin sama sun tarwatsa wata tawaga ta kusan ’yan bindiga 300 da ke tafiya a kan babura bayan samun bayanan […]
Rundunar sojojin Operation FANSAN YAMMA ta ce, sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ’yan bindiga mai suna Alhaji Tukur a Zamfara, tare da daƙile hare-hare a Zamfara da Katsina.
Rundunar ta kuma ce samamen jiragen yaƙin sojin sama sun tarwatsa wata tawaga ta kusan ’yan bindiga 300 da ke tafiya a kan babura bayan samun bayanan sirri.
- Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa
- Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi
A cewar rundunar, lamarin ya hana maharan kai hare-haren da suka shirya kan wasu unguwanni.
Samamen waɗanda aka gudanar a ranar 7 ga watan Yuli, sun biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma farmakin da dakarun ƙasa suka ci gaba da kaiwa tare da tallafin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), kamar yadda ya fito a cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Haɗin Gwiwar Rundunonin Tsaron, Kanal Aliyu Danja ya fitar a ranar Talata.
A Jihar Zamfara, dakarun ƙarƙashin Sashe na 2, tare da haɗin gwiwar dakarun sa-kai na tsaron cikin gida, sun mayar da martani ga bayanan sirri da ke nuni da wani hari da ke shirin aukuwa a wasu yankuna na ƙaramar Hukumar Kaura Namoda.
Dakarun sun fuskanci ’yan ta’addan a wata mummunar fafatawa ta musayar harbe-harbe, inda suka yi nasarar fatattakar harin tare da tilastawa maharan ja da baya bayan an kakkaɓe wasu daga cikinsu.
A wani farmaki makamancin haka da aka gudanar a kewayen Dogon Kade, dakarun da suka kai ɗauki lokacin da aka kai wa manoma hari, sun yi nasarar hallaka wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga mai suna Alhaji Tukur, wanda aka ce ƙanin babban jagoran ’yan fashi ne da ake nema ruwa a jallo, wato Alhaji Shehu Bagiwaye.