Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunsu na ‘Operation Lafiya Dole’ da ke yakar ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe kwamandoji biyu a yankin Arewa maso Gabas yayin wani samame da suka kaiwa ‘yan kungiyar a Borno. Sojojin sun ce, kwamandojin biyu da aka kashe su ne Abu Rajal da Tuja Sa’inna Banki. An samu nasarar […]
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunsu na ‘Operation Lafiya Dole’ da ke yakar ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe kwamandoji biyu a yankin Arewa maso Gabas yayin wani samame da suka kaiwa ‘yan kungiyar a Borno.
Sojojin sun ce, kwamandojin biyu da aka kashe su ne Abu Rajal da Tuja Sa’inna Banki.
An samu nasarar kashe kwamandojin ne ta hanyar bhagdin gwiwar jami’an tsaro na bataliya 25 da ke sansanin Chibok da kuma bataliya ta 28 da ke sansanin sojoji a Dambuwa ranar 9 ga Nuwamba 2018.