Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP 3 da mayaƙa 22 a Borno

Manyan shugabannin ISWAP da mayaƙa da dama sun halarci jana’izar mamatan a ranar Litinin.

Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP 3 da mayaƙa 22 a Borno

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe wasu manyan kwamandojin Ƙungiyar ISWAP uku da mayaƙanta 22 a Jihar Borno.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da sojojin rundunar Operation Hadin Kai ta sojin saman ta kai wa sansanin mayaƙan a Karamar Hukumar Marte a jihar ta Borno.

Ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce harin na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai farmaki wani ƙauye mai nisa da ke Arinna Woje a Yammacin ranar Lahadi.

Majiyar Zagazola Makama ta ce, jiragen saman sojin sun kai jerin hare-haren ne babu kakkautawa, lamarin da ya kai ga halaka mayaƙan da dama.

Ya ce daga baya an tsinto gawarwakin kwamandojin ’yan ta’addan uku da suka haɗa da Abacha da Bakura, sai Babangida da kuma wasu masu mayaƙa 22, waɗanda tuni an yi jana’izarsu a Yammacin ranar Litinin.

Majiyar ta ƙara da cewa, daga cikin manyan shugabannin ISWAP da suka halarci jana’izar akwai Abu Nazir da Abu Rijal da Khalid na Kolaram da sauran mayaƙa da dama.