Sojoji sun kashe Lakurawa a Sakkwato

Dakarun sojin Rundunar Operation Fansan Yamma sun bindige wasu ’yan ta’addan Lakurawa biyu har lahira, bayan hare-haren ’yan ta’adda a sansanin Hukumar Shige da Fice ta Najeriya. Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya sanar a ranar Juma’a cewa ’yan ta’addan sun yi yinƙurin ƙona wani ofishin Hukumar Shige da […]

Sojoji sun kashe Lakurawa a Sakkwato

Dakarun sojin Rundunar Operation Fansan Yamma sun bindige wasu ’yan ta’addan Lakurawa biyu har lahira, bayan hare-haren ’yan ta’adda a sansanin Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.

Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya sanar a ranar Juma’a cewa ’yan ta’addan sun yi yinƙurin ƙona wani ofishin Hukumar Shige da Fice da ke ƙauyen Ruwa Wiri a Ƙaramar Hukumar Tangaza, amma sojoji suka kai wa ofishin ɗauki bayan samun kiran gaggawa.

Osoba ya ce sojojin sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan, inda suka kashe biyu daga cikinsu, sauran kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Ya kara da cewa, binciken da aka yi a yankin ya kai ga gano bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai da kuma babur da ’yan ta’addan suka yi amfani da shi wajen guduwa.

Osoba ya ce, a wani samame na daban da aka kai a Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina kuma, sojoji sun tare wasu ’yan ta’adda da ke tafiya da dabbobin da suka sace a ƙauyen Danya Bakwai.

Ya ce sojojin sun yi artabu da su, inda suka tilasta musu barin dabbobi 62 da aka sace, daga bisani aka mayar da su ga masu su a fadar Hakimin Daddara.

Osoba ya jaddada cewa rundunar tana ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Arewa maso Yamma, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba hukumomin tsaro bayanan sirri masu inganci.