Sojoji sun kashe manyan ’yan ta’adda 5 a Kebbi
Sojojin sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka yi artabu da maharan kafin daga bisani su yi galaba a kansu
Sojoji sun kashe aƙalla biyar daga cikin fitattun jagororin ’yan bindiga biyar da suka addabi wasu ƙauyuka a Jihar Kebbi, a wani samame da suka kai da sanyin safiyar ranar Juma’a.
Majiyoyin soji sun shaida wa wakilinmu cewa an kashe ’yan bindigar ne lokacin da suke ƙoƙarin kai hari ƙauyen Kangiwa domin yin garkuwa da mazauna yankin.
Majiyar ta ce sojojin sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka yi artabu da maharan kafin daga bisani su yi galaba a kansu.
“Da safiyar yau ne aka gudanar da wani babban samame a ƙauyen Kangiwa da ke Jihar Kebbi. A yayin aikin, an kashe wasu manyan shugabannin ’yan bindigar da suka daɗe suna addabar yankin.
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 4 a Zamfara
- ’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun masu garkuwa a Kaduna
- Gwamnatin Tinubu za ta yi ƙarin albashi mafi ƙaranci na N70,000 — Gbajabiamila
“Har yanzu ba mu da cikakken adadin waɗanda aka kashe, amma zan iya tabbatar da cewa aƙalla mutum biyar daga cikinsu sun mutu.
“Yawancin gawarwakin da aka gani na manyan shugabannin ƙungiyar ne. An kashe su ne a wani mummunan artabu da ya ɗauki kusan awa biyu,” in ji majiyar.
Ta ƙara da cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya samu rauni a yayin aikin.
A cewarta, bayan kammala samamen, sojojin sun ci gaba da binciken yankin domin tabbatar da cewa ba a binne nakiyoyi ba.
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na kafafen sada zumunta.
Ya ce, “Da sanyin safiyar Juma’a, 26 ga Yunin 2026, jami’an tsaro sun yi nasarar kashe adadi mai yawa na ’yan bindiga masu ɗauke da makamai a wani samame da suka kai ƙauyen Kangiwa da ke Jihar Kebbi.
“Allah Ya ci gaba da bai wa jami’an tsaronmu nasara tare da kare su yayin da suke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro.”
Da aka nemi jin ta bakin Rundunar Sojin Nijeriya, kakakinta, Kanar Appolonia Anele, ta ce za ta bayar da cikakken bayani daga baya.
Wannan samamen na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar0Janar Waidi Shuaibu, ya umarci dakarun da su ƙara kaimi wajen fatattakar duk masu ƙoƙarin tayar da zaune tsaye a faɗin ƙasar.