Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji
Dakarun sojin sun kuma kashe wasu daga cikin kwamandojin Turji a hare-hare daban-daban.
Dakarun Sojin Operation Hadarin Daji, sun kashe Aminu Kanawa, Mataimakin Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, a wani samame da suka kai a Jihohin Zamfara da Sakkwato.
Hare-haren da dakarun suka kai ta sama da ta ƙasa, ya yi sanadin raunata ɗan uwan Bello Turji, mai suna Dosso.
- Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda
- ‘Nan da shekaru 2 za a nemi likitoci a rasa a Nijeriya’
Har ila yau, sun kashe wasu abokansa da suka haɗa da Suleiman, wanda yake jagorantar tawagar da ke ƙoƙarin ceto sansanin Turji.
Samamen, wanda aka kai a ranar 20 zuwa 21 ga watan Janairu, ya shafi yankunan Shinkafi, Fakai, da Gebe a Jihohin Zamfara da Sakkwato.
Sama da ’yan ta’adda 24 aka kashe, kuma dakarun sun lalata wata makarantar firamare da ’yan ta’addan suka mayar wajen ajiye makamansu.
Wannan nasara ta rage tasirin maharan sosai, ta hana su damar tsara hare-hare a nan gaba.
Darakta yaɗa labaran rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa sojojin sun kashe wasu manyan shugabannin ƙungiyar Turji; kamar Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, da Ɗan Kane.
A cewarsa, a yayin hare-haren, an yi wa maharan luguden wuta, inda aka lalata maɓoyarsu a Zamfara da Sakkwato.
Hare-haren na daga cikin dabarun sojojin na kawo ƙarshen ’yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Gwamnatin Tarayya, ta nemi haɗin kan jama’a, da suke bayar da bayannan sirri da za su taimaka wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga.
Haka kuma, hukumomi na binciken hanyoyin da za su daƙile hanyar da mahara za su samu maɓoya.
Sojojin sun jaddada aniyarsu ta tabbatar da samar da yanayin zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
Sojoji za su ci gaba da mayar da hankali kan kawar da barazanar ta’addanci, domin dawo da zaman lafiya.