Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12 a Borno
Sojojin sun kuɓutar da wasu mutane 16 waɗanda suka haɗa da mace ɗaya da yara 15.
Dakarun Operation Haɗin Kai sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 12 a wani farmaki da suka kai wa mayaƙan a gabar dajin Sambisa.
Kamar yadda Zagazola Makama, ƙwararren mai sharhi kan sha’anin tsaro a Tafkin Chadi ya bayyana, dakarun sun kai farmaki ne a ranar 9 ga watan Agusta, 2024.
- Hotunan yadda aka gudanar da addu’o’i kan matsin rayuwa a Kano
- Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 a wata makaranta a Gaza
Makama ya ce dakarun haɗin gwiwa da suka lokacin da na Operation Haɗin Kai, Desert Sanity III kuma rundunar Hybrid Force ne suka ka yi wa mayaƙan dirar-mikiya a yankunan Bula Dalo, Bula Marwa, Gaizuwa, da Chongolo da ke Ƙaramar Hukumar Bama a Jihar Borno.
Majiyoyin leƙen asiri sun ƙara da cewa, wannan kwantan ɓaunar da sojojin suka ya sanya mayaƙan suka tsere daga yankin.
Majiyar ta ƙara bayyana cewa, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 12, yayin da aka ƙwato wata nakiya (IED) guda ɗaya, da bindigogin AK-47 guda uku, da keke ɗaya, da tutocin ƙungiyar ta Boko Haram guda uku, da kuma magunguna.
Bugu da kari, sojojin sun kuɓutar da wasu mutane 16 waɗanda suka haɗa da mace ɗaya da yara 15.