Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 42 a Biu
Akalla maharan da ake zargi ’yan Boko Haram 42 ne ciki har da ’yan kasar Chadi 15 ne sojoji suka yi musu kwanton bauna suka kashe su a lokacin da suke kokarin kai hari ga barikin soja na Biu da ke Jihar Borno. Majiyoyi sun ce daruruwan sojoji da matasa ’yan banga da suka samu […]
Akalla maharan da ake zargi ’yan Boko Haram 42 ne ciki har da ’yan kasar Chadi 15 ne sojoji suka yi musu kwanton bauna suka kashe su a lokacin da suke kokarin kai hari ga barikin soja na Biu da ke Jihar Borno.
Majiyoyi sun ce daruruwan sojoji da matasa ’yan banga da suka samu labarin zuwa maharan da misalign karfe 7:30 na safe ta hanyar Gombi a kusa da matsugunin sojojin sun samu nasarar kashe maharan 42 yayin da dama suka gudu da raunuka.
Bayanai sun ce mazauna Biu sun firgita lokacin da suka ji karar fashewar bam, lamarin da ya sa da dama suka ranta a na kare.
Wani dan kasuwa mai suna Mohammed Aliyu ya ce, “Sojojin sun samu nasara ba wa maharan kashi, wadanda aka yi musu kwanton bauna.
Biu, da ke da nisan kilomita 200 daga Maiduguri fadar Jihar Borno shi ne gari mafi girma a Kudancin Borno kuma ya rika tsallake hare-hare da dama da Boko Haram suka kai don kwace garin a ’yan watannin nan.
Mohammed Aliyu ya ce, “An kwato miyagun makamai ciki har da tankar yaki daga maharan.”
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta dakile wani hari da ’yan Boko Haram suka kaddamar a garin na Biu.
Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa BBC cewa rundunar ta yi nasarar fatattakar ’yan Boko Haram tare da damke mayakan kungiyar biyar da kuma motocinsu.
Wani mazaunin garin a hirarsa da BBC ya ce an kashe ’yan Boko Haram shida a lamarin, sannan mota daya tal ta ’yan Boko Haram aka ga ta koma sansaninsu daga cikin motocin 11 da aka ga sun nufi garin Biu da safiyar ranar shekaranjiya Laraba.
“Da misalin karfe 7:00 muka fara jin karar harbe-harbe daga nan sai ’yan Boko Haram suka kona caji ofis na ’yan sanda,” in ji wani mutumin Biu.
Ya kara da cewa “Sojoji da ’yan Sibiliyan JTF sun hana su (Boko Haram) shiga Biu sannan aka ci karfin ’yan Boko Haram, kuma na ga gawarwakin ’yan Boko Haram a kan wasu hanyoyi.”
Bayanai sun nuna cewa garin Biu shi ne kadai gari a yankin Kudancin Borno da ba ya karkashin ikon ’yan Boko Haram.