Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 63 a Borno

Sojoji sun kashe mahara 63 a farmaki biyu da suka kai ta sama da kasa a Jihar Borno bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai ga matsugunin soja.A ranar 20 ga Disamban da ya wuce ne mayakan da ake ji na Boko Haram ne suka kai hari ga Bataliyar Sojojin Tanka ta 202 da […]

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 63 a Borno

Sojoji sun kashe mahara 63 a farmaki biyu da suka kai ta sama da kasa a Jihar Borno bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai ga matsugunin soja.
A ranar 20 ga Disamban da ya wuce ne mayakan da ake ji na Boko Haram ne suka kai hari ga Bataliyar Sojojin Tanka ta 202 da ke Bama inda suka halaka sojoji 15, kuma Hedkwatar Tsaro ta ce, an kashe maharan da dama lokacin da aka ba sawunsu.
Hedkwatar Tsaro ta kasa da Runduna ta Bakwai ta Sojan Najeriya da ke Maiduguri suka bayyana a yawan wadanda aka kashe a harin na baya-bayan nan a sanarwa daban-daban da suka fitar.
Daraktan Labarai na Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade, ya ce a harin sama da kasa da aka kai a dajin Alafa da ke nisan kilomita 21 daga Bama, an kashe ’yan bindiga 56, yayin da sojoji biyu suka samu rauni.
Ya kara da cewa wasu bakwai daga cikin ’yan bindigar a wata fafatawa da rundunar hadin gwiwa na kasashen da ke iyaka da Najeriya a kusa da iyakar Nijar da Chadi.
“Bisa aiki da rahotannin sirri da suka gano ’yan ta’adda na yunkurin kafa sabon sansani a dajin, harin sama da kasa da aka kai sun yi mummunar illa ga maharan inda suka rasa dimbin mutane da kayan aiki,” inji Olukolade.
Ya kara da cewa “Kai harin bama-bamai ta kasa da sama na ci gaba a wurare da dama a inda aka ba rahoton an ga ’yan ta’addan. A gefe daya sojojin rundunar hadin gwiwa sun bata wani yunkuri na ’yan ta’addan da suke kai-kawo a yankin Tafkin Chadi da suka yi yunkurin kai hari ga wasu al’ummomin Najeriya. Bakwai daga cikin ’yan ta’addan sun mutu, yayin das aura suka gudu ta sassa daban-daban wasu Jamhuriyar Nijar wasu Chadi kuma sojoji suna farautarsu. Rahotannin sirri sun tabbatar da cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan da aka raunata an gan su a cikin kwale-kwale sun nufi garin Tumbun Telkandam da ke Jamhuriyar Chadi.”
A wata sanarwa ta daban, mukaddashin kakakin Ruduna ta Bakwai Kyaftin Aliyu Ibrahim Danja, ya ce “Sojojin Runduna ta Bakwai tare da tallafin sojojin sama na Najeriya sun kai hari ga ’yan Boko Haram da suke yankin dajin Alafa da jijjifin ranar Asabar 28 ga Disamban bara. Fiye da mayaka 56 aka kashe a yayin fafatawar inda da dama suka gudu da raunukan harbin bindiga. Sannan sojojin sun lalata makamai da kayayyakin aiki da motocin ’yan ta’addan a yayin harin na kasa da sama, inda sojoji biyu suka samu rauni.”
Kyaftin Danja ya ce kai farmakin wani bangare ne na aikin da sojojin ke yi domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara lafiya a Jihar Borno.
‘Kwamandan Runduna ta Bakwai ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar Obidah Ethan, na taya al’ummar Jihar Borno murna, kuma yana bukatar su taimaka wa sojojin da bayanai masu amfani. Wannan zai taimaka sosai tare da saukaka musu wajen gudanar da ayyukansu a kokarinsu na kare rayuka da dukiya a Jihar Borno,” inji shi.
Farmakin na baya-bayan nan ya biyo bayan miyagun hare-hare guda biyu da aka wa matsugunnan sojoji a Maiduguri da Bama.
Mayakan Boko Haram sun kai hari ga rukunin soja na 79 na sojojin birged din Atilare na 333 da kuma wani ofishin hedkwatar shiyya na ’yan sanda a ranar 2 ga Disamban da ya gabata. A yayin harin an lalata jiragen sama na yaki na sojoji guda biyar da kuma wasu gine-gine, amma mahukunta sun ce ba wanda ya rasa ransa a bangaren jami’an tsaro.

… Wadanda suka mutu a harin bikin aure sun kai 12

Daga Hamza Idris, Maiduguri da Salihu Makera

Yan bindiga da aka zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun auka wa wani wurin bikin aure a karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno inda suka halaka mutum takwas nan take tare da raunata 12, wadanda hudu daga cikinsu suka cika a asibiti daga baya.
Shaidu sun ce maharan su biyu, sun je wurin bikin ne da ake yi a kauyen Tashan Alade da ke kan hanyar Bama zuwa Gwoza a ranar Asabar a kan babur inda suka nuna kamar su ma bakin bikin ne.
Wani bako a wurin bikin daga Sokwa da ke kusan da kauyen mai suna Sama’ila Ali ya ce maharan sun shammaci masu bikin wajen karfe 2:00 na rana lokacin da ake watsa takarduh Naira ga ma’auratan. “Sun bude wuta ga mutanen da suke rawa  a wurin da ake gudanar da bikin… mun ji karar harbe-harben bindiga, inda daukacin wurin ya rude kowa ya waste baya ga wadanda aka kashe ko aka raunata,” inji shi.
Ali wanda ya tattauna da wakilinmu ta tarho bai iya tabbatar da ko harin ya ci ran ango da amaryar ba.
Wani mazaunin Maiduguri ya shaida wa Aminiya a ranar Lahadi cewa kawunsa mai suna Yusuf Dauda na cikin mutum takwas da aka kashe.  Ya ce marigayi Dauda ya bar Maiduguri zuwa Tashan Alade ne da niyyar halartar bikin auren wanda ya samu halartar ’yan uwa da abokan arziki daga sassa da dama.
“Kamar mahaifiyar Yusuf ta san zai mutu, domin ta kira shi mintoci kadan kafin a kashe shi. Lokacin da ya shaida mata cewa an kammala daura auren a coci, ta ce masa kada ya bata lokacinsa a sauran bukukuwan, amma abin bakin ciki, daga baya sai aka shaida mata cewa danta ya rasu,” inji shi.
Majiyoyin asibiti da iyalan wadanda harin ya rutsa da su sun shaida wa wakilinmu a ranar Litinin da ta gabata cewa, wadanda suka mutu sun kai 12.
Monica James wanda dan uwanta ya cika a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ta ce sun kadu game da harin wanda ta ce an kai shi ne ba tare da wani dalili ba. “dan uwana yana cikin mutum biyar da suka cika daga baya,” inji ta. Sai dai majiyar asibitin ta ce,  “Daga cikin mutum hudun da suka mutu biyu suna dauke da harbin bindiga a kirji da kugunsu, yayin da saura biyun suka mutu sakamakon yawan zuban jini.”  
A wani harin na daban da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai a ranar Juma’ar da ta gabata, maharan sun yi wa mutane da dama yankan rago tare da kone gidaje sama da 30 a kauyen Warabe da ke kusa da Pulka da bai da nisa da dajin Sambisa da ke karamar Hukumar Bama.
Mohammed Babagan wani direba da ya wuce ta kauyen a ranar Lahadin da ta gabata ya ce, “Mutanen kauyen suna dandana kudarsu sosai a hannun ’yan ta’addan.”
Ya ce, “Mutane kalilan ne suka rage a wurin yanzu, galibinsu mata da yara. Na dauko wasu dangin wadanda harin ya shafa wadanda suka je can domin ta’aziyya, kuma da ni aka yi musu Sallah,” inji shi.
Ya ce  wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su suna cunkushe ne a gidajen da suka saura a kauyen.
Lokacin da aka tuntubi kakakin Runduna ta Bakwai ta Sojan Najeriya da ke Maiduguri Kanar Mohammed Dole ta waya ya nemi wakilinmu ya tuntubi Kyaftin Aliyyu Danja, wanda kuma aka kasa samunsa zuwa lokacin rubuta labarin.
Sojojin da suke aikin tsaro a hedkwatar Runduna ta Bakwai sun ce Danja ya fita wani aiki na musamman ne.