Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 11 a dajin Sambisa

An kashe mutanen ne a dajin Sambisa

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 11 a dajin Sambisa

Mayakan ISWAP

Dakarun Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar dakarun farar hula na sa kai Civilian Joint Task Force (CJTF) da dakarun hadin gwiwa sun kashe yan ta’addar ISWAP 11.

An kashe ’yan ta’addan ne a wani mummunan hari da suka kai a cikin dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

’Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da jami’an leken asirin suka kai farmaki a tsakanin ranar 31 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yunin 2023.

An kai harin ne a maboyar ’yan ta’addan da ke cikin yankin Karamar Hukumar Damboa da Chibok a dajin na Sambisa.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa sojojin sun kai farmaki tare da lalata wasu maboyar ’yan ta’addan a Bale, Tirke, Mandari, Molgoi, Bego, Yarwa da Ngurna.

Ya ce an samu nasarar kwato wasu makamai da alburusai da sauran kayan aiki yayin aikin hadin gwiwar sojojin da sibiliyan JTF.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja