Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP 5 A Borno
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe mayakan kungiyar ISWAP a Jihar Borno.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe mayakan kungiyar ISWAP a Jihar Borno.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wani harin kwantan bauna da sojojin bataliya ta 3 tare da hadin gwiwar mayakan sa-kan CJTF a ranar Lahadi.
Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun kai harin ne a Moula, ind ake zargin ’yan tada kayar bayan ke hada kayan aikinsu a Ngala.
A wata mai kama da hakan kuma, sojojin bataliya ta 202 da aka girke a Bama sun kashe wani dan ta’adda a safiyar ranar Litinin.
Dan ta’addan ya yi yunkurin kai wa sojojin hari ne a cikin duhu, amma suka aika shi lahira ba tare da bata lokaci ba.