Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

An kashe Alhaji Ma’oli ne tare da wasu da ake zargin ‘yan tada ƙayar baya ne a ranar Alhamis.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa

Rundunar Sojojin haɗin gwiwa ta birged na 1 na dakarun Operation Fansan Yamma, a Arewa maso Yamma sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga Alhaji Ma’oli a Jihar Zamfara.

An kashe Alhaji Ma’oli ne tare da wasu da ake zargin ‘yan tada ƙayar baya ne a ranar Alhamis.

Kakakin jami’an tsaron haɗin gwiwar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya ce samamen da ya yi sanadin mutuwar Alhaji Ma’oli da na wasu ya faru ne a ƙauyen Mai Sheka da ke kusa da garin Kunchin Kalgo “wanda ɗaya ne daga cikin al’ummar yankin da ake ƙuntata wa kuma suke shan wahala daga Ma’oli”.

“Ma’oli ya yi suna a kullum ta hanyar ƙaƙaba wa mazauna unguwannin harajin da ba bisa ƙa’ida ba ga Unguwan Rogo, Mai Sheka, Magazawa, da sauran yankunan da ke kewaye da Bilbis a ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara,” in ji Abdullahi a wata sanarwa a ranar Juma’a.

A cewarsa, mutuwar Ma’ oli ta “samar da kwanciyar hankali da farin ciki ga mazauna yankin Bilbis”.

Ya ce, wannan farmakin ya biyo bayan rahoton sirri da aka samu game da ayyukan ‘yan tada ƙayar bayan a kan babura da ke aiki a yankin Bilbis da ke gundumar Bilbis a Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara