Sojoji sun kashe shugabannin ’yan bindiga 65 da mayaƙa 1,937 a watanni uku

Sojojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda 339.

Sojoji sun kashe shugabannin ’yan bindiga 65 da mayaƙa 1,937 a watanni uku

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kashe shugabannin ’yan bindiga 65 da ɗaruruwan mayaƙa a ƙasar bayan sabbin hare-hare da aka kai a watanni uku na wannan shekarar.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Manjo Janar Buba ya ce “Farmakin da dakarunmu suka kai a tsakanin watan Yuli da Satumba sun yi sanadiyar kashe manyan shugabannin ’yan ta’adda 65.

“A watanni uku na wannan shekarar, dakarunmu sun kawar da ’yan ta’adda 1,937.

“Sun kama ’yan ta’adda 2,782 da kuma wasu masu aikata manyan laifuka tare da kuɓutar da mutane 1,854 da aka yi garkuwa da su,” in ji Buba a sanarwar da ya fitar.

’Yan bindigar da sojojin suka kashe sun haɗa da ’yan ta’addar Boko Haram, mayaƙan Daular Musulunci ta Yammacin Afirka, da ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da dama.

Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Halilu Sububu, wanda sojoji suka taɓa bayyana cewa suna neman sa ruwa-a-jallo a 2022 tare da saka diyyar naira miliyan biyar ga duk wanda ya faɗi inda yake.

Sauran waɗanda dakarun ƙasar suka samu nasarar kashe wasu manyan kwamandojin ’yan bingida da suka haɗa da Munzir Arika da Sani Dilla (Ɗan Hausawan Jubillaram) da Ameer Modu da Ɗan Fulani Fari Fari Dungusu da Abu Darda da kuma Bakoura Arina Chiki.

Sauran sun haɗa da Dungusu da Abu Darda da Abu Rijab da Matawal Bitrus da Thomas Benedict da Mohammed Sani da Rimamy (Omo) da Terkimbi Injoko da Jacob Uzege da Ibn Kasir da Kachalla Dan Baleri da Kachalla Dan Ali Garin Fadama da Kachalla Basiru Zakarriya da kuma Ofem Emmanuel Igwe.

Haka kuma, sanarwar ta ce an kama wasu da ake zargi da kasancewa ’yan bidigar kimanin 606 tsakanin waɗannan watanni tare da kuɓutar da mutum 476 da ake garkuwa da su, sannan kuma wasu iyalan ƴanbindigar kimanin 7,283 suka miƙa wuya.

Sanarwar ta kuma ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda 339, da ƙirar gida 58 da ƙananan bindigogi 83 da kuma tarin alburusai.

A farkon watan Satumba, Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni ga Ministan Tsaro da manyan kwamandojojin soji da su koma Jihar Sakkwato da ke Arewa maso-Yamma, ɗaya daga jihohin da ta’addanci ya yi ƙamari, domin su yaƙi ta’addanci.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano