Sojoji sun kashe Halilu Sububu ubangidan Bello Turji a Zamfara

Sojojin sun samu nasarar ce bayan ɗauki ba daɗi da ’yan bindiga.

Sojoji sun kashe Halilu Sububu ubangidan Bello Turji a Zamfara

Dakarun sojojin Nijeriya sun samu nasarar kashe kasurgumin ɗan fashin daji, Kachalla Halilu Sububu a safiyar Juma’a.

Kafin kisan nasa, Kachalla ya kasance ubangidan ɗaya daga cikin manyan ’yan ta’addan nan Bello Turji.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana haka a shafins na Facebook.

Sojojin dai sun samu nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne bayan ɗauki ba daɗi tsakaninsu da ’yan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanki a ƙananan hukumomin Moriki da Anka da ke Zamfara.

Hadimin Shugaban Ƙasar ya ce, “wannan wata ƙarin nasara ce bayan kashe wasu jiga-jigan ɓarayin daji da aka yi a cikin shekara ɗaya da ta gabata.

“Waɗanda aka samu aikawa lahira a cikin wannan lokaci sun haɗa da Kachalla Ali Ƙawaje (ƙasurgumin ɗan ta’adda da ya taɓa harbo jirgin soja a Kaduna), Damina (mutumin da ya addabi yankin Ɗansadau), Moɗi-Moɗi, Ɓaleri (wanda ya sace ɗaliban Kaduna), Ɗangote, da sauransu.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato