Sojoji sun kashe wani ango a kan wayar salula
Iyayen wani matashi dan shekara ashirin da biyar , mai niyyar aure kwanannan, mai suna Ahmadu Yahaya wanda ya rasa ransa a hannun sojoji a sakamakon azabtar da shi da suka yi saboda wai an samu wayar salular budurwar daya daga cikin sojojin a hannunsa sun bukaci a biya su diyyar kashe musu da da […]

Iyayen wani matashi dan shekara ashirin da biyar , mai niyyar aure kwanannan, mai suna Ahmadu Yahaya wanda ya rasa ransa a hannun sojoji a sakamakon azabtar da shi da suka yi saboda wai an samu wayar salular budurwar daya daga cikin sojojin a hannunsa sun bukaci a biya su diyyar kashe musu da da aka yi.
Aminiya ta gano cewa, al’amarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Mayu na wannan shakarar a unguwar Sanusi da ke Kaduna. Haka kuma bayanai sun nuna cewa marigayin da aka fi sani da Madu, sana’ar kafinta yake yi.
A cewar yayan mahaifin marigayin, Malam Adamu Mohammad, mai shekaru sama da 70, wanda kuma tsohon ma’aikacin Barakin Sojoji ne na One Dib da ke Kawo Kaduna, ya ce a gabansa sojojin suka kama matashin a ‘yar kasuwa a Unguwar Sanusi.
Ya ci gaba da cewa,marigayin yana zaune a kan dakali ne lokacin da sojoji uku suka zo a mota kirar Golf suka kama shi suka saka shi cikin butt na motar suka tafi da shi.
“ Lokacin da suka kama shi ni kuma sai na taso domin in tambaye su dalili da kuma ko laifin mai ya yi musu, amma kafin in karaso wajensu sai daya daga cikinsu ya auna ni da bindigarsa kamar zai harbe ni, ya kuma nemi da kada in karaso kusa da su. Ganin haka sai na tsaya nesa. Sai kawai suka dauke shi suka saka a cikin butt na mota yana ihu suka wuce da shi.Daga bayan ne sai muka samu labarin wai a kan wayar salula aka kama shi.’’
“ Amma mun samu labarin cewa wai marigayin ya hada neman budurwa ne da daya daga cikin sojojin da suka kamashi kuma wai budurwar ce ta bai wa marigayin wayar salular da ta yi sanadiyyar rasuwarsa,” inji shi.
Binciken da Aminiya ta yi ta kuma gano cewa, sojojin da suka kama shi su uku ne kuma sun kai shi ofishinsu ne da ke Bakin ruwa, Rigasa, inda suka yi ta azabtar da shi har sai da ya mutu .
Rahotanni sun kuma nuna cewa marigayin ya samu karaya a wuyarsa, sannan hannu da kafufunsa duk sun kumbura saboda mugun daure shi da suka yi.
“Ni na yi masa wanka kafin a kai shi makabarta kuma gaskiya abin babu kyan gani, domin hannunsa da kafafunsa duk sun kumbura sannan kuma wuyansa a murde yake. Kuma kafadarsa ma akwai rauni mummuna,’’ inji Malam Adamu.
Wakilinmu ya kuma samu zantawa da Mahaifin marigayin, Malam Yahaya Muhammad inda ya bayyana masa cewa, da daddare ya samu labarin kamun dan nasa. A cewarsa, sojojin ne suka kira shi a wayarsa cewa ya je ya same su ko kuma su aika da yaronsa inda ba zai sake dawowa ba.
“ Duk abin da ake yi ban sani ba sai da misalin karfe 9 na dare. sai mahaifiyarsa take fada min cewa ai sojoji sun kama Ahmadu, kafin ta gama fada min sai suka kira ni a wayata cewa in je in same su ko kuma su kai Ahmadu inda ba zai sake dawowa ba. Jin haka sai ni da yayansa muka karasa wajensu. Ko da isarmu bakin kofar shiga sai na rika jin ihun Ahmadu, ga alarma suna bugunsa.
“ Ina shiga ciki sai na ganshi a daure sun yi masa mugun dauri. ganinmu sai ya fara ihu yana cewa, in taimake shi kar su kashe shi. Gaskiya sun yi masa mugun dauri a hannunsa da kafafunsa. Da na ga haka sai na tambaye su laifin me ya yi haka suke dukansa? babu wanda ya ce da ni wani abu, sai dai kawai suka ce wai maganar ta wayar salula ce. Sai daya daga cikin sojojin ya ce da shi ya nemi gafarata. Sai na tambayeshi mai yake nufi da haka? amma sai ya ce dole sai yaro ya nemi gafara ta. Daga nan sai na ce to na yafe masa duk abin da ya yi min.’’
“ Daga nan sai suka ce da ni in tafi gida washegari in dawo in karbe shi. Sai na roke su da su kwance masa daurin da suka yi masa. Ko da suka kwance masa hannu da kafa kasa mikewa tsaye ya yi. Da ya yunkura sai ya fad,i yana kuka yana cewa da ni, kada in barshi a wajensu domin za su kashe shi. Ban bar wajen ba sai da suka tabbatarmin da cewa ba za su sake dukansa ba,” inji shi.
Ya ce, da safe bayan ya koma domin ya karbo dan nasa sai ya tarar da shi da sojojin an kwashe su daga wajen. Wadansu ya gani a wajen, da ya tambaye su sai aka ce masa ai an kai yaron ne domin yin karin kummallo, saboda haka ya je ya dawo.
“ Da misalin karfe uku na rana sai ga sojoji a gidana wai sun zo wajena. Daga nan ne suka fara ba ni hakuri wai ai dana Allah Ya yi masa rasuwa.Akwai wani Kanar Abdullahi a cikinsu shi ne wanda yake ta ba ni baki a kan in yi hakuri. Suka bukaci wai za su yi masa wanka na ce a’a su kawo min dana in ganshi,” inji mahaifin cikin kuka.
Sojojin sun kai masa gawar yaron nasa ne da misalin karfe 5 na yamman ranar domin a yi masa situra, kuma su sojojin ne da kansu suka kai wa iyalansa lufafar da aka yi amfani da ita wajen rufe shi. “ Sun kuma bamu naira dubu dari cewa mu yi amfani da shi wajen yi masa addu’a. sannan sun neme mu daga baya a kan mu je mu yi bayani a rubuce a hedikwatar rundunar sojoji ta daya da ke Kawo Kaduna. Mun kuma yi yadda suka bakuci mu yi,’ inji shi.
Da wakilinmu ya tambayeshi ko me yake so a yi masa, sai ya ce, “ da dai harbinsa suka yi a bisa kuskure da sai in ce na yafe, amma wannan abin da aka yi masa ganganci ne, a ce wai saboda wayar salula kawai a kashe min yaro, dole sai na bi hakkina, idan kuma sun ki sai in barsu da Allah,’’ inji shi cikin hawaye.
“ Ni ba ina kuka bane saboda rasurwarsa, a’a na sani kowace rai mamaciyace. Ina kuka ne kawai saboda na ga irin azabar da ya sha a hannunsu kafin rasuwarsa, saboda haka ina neman a biya mu diyya,” inji shi.
Bayanai sun nuna cewa, lokacin da sojojin suka kai gawarsa gidansu da ke layin PRP, Hayin Rigasa, da yawansu suka je kuma rike da makamai domin gudun ko-ta-kwana saboda an ce matasa sun yi cincirindo domin daukar fansa. Amma dattawa suka hana su.
Akwai bayanai da suka nuna marigayin na shirin yin aure nan bada dadewa ba kafin abin ya faru.
Aminiya ta samu labarin cewa, sojojin da ake zargi da aikata laifin su uku ne kuma tuni aka tsare su a kurkuku da ke hedikwatar rundunar sojoji ta daya da ke kawo, Kaduna .
kokarin da wakilinmu ya yi domin zantawa da yarinyar da aka ce ita ta bai wa marigayin waya ya ci tura, domin babu wanda ya san gidansu. Sai dai an ce tana zaune ne a Hayin Rigasa.
Kakakin rundunar sojojin da ke Kaduna, Kanar Sani Kukasheka ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya nuna cewa rundunar na bincike kuma da zarar an kammala za a hukunta sojojin.
Kuma akwai wani lauya mai kare hakkin dan Adam, mai suna Barista Sadau Garba, da ke kan gaba wajen ganin an kwato wa iyalan hakkinsu.“ Muna bin kadin wannan cin zalin da aka yi wannan bawan Allah. Sai mun kwato masa hakkinsa da yardar Allah,” inji shi.