Sojoji sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram a Borno

An kashe shi ne tare da wasu mayaka a harin sojoji ta sama

Sojoji sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram a Borno

Wasu sojojin Najeriya

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ’yan ta’adda ya Boko Haram, Abu Asad a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno.

Sojojin sun samu nasarar ce a wani hari da suka kai ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023, kan wasu tarin ’yan ta’adda a wani kebabben wuri da ya kunshi tsaunin na Mandara cikin Jihar ta Borno.

A cewar Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, wani faifan bidiyo ya nuna ’yan ta’addan na taruwa a wurin domin shirin kai kwani gagarumin hari kan dakarun nasu.

Sama da ’yan ta’adda 100 dauke da muggan makamai ne aka ga wasu dakarun suna ta zagaya su a tsakanin itatuwa dauke da bindigogin harbo jirage.

Edward ya ce ganin hakan ne ya sa suka kai musu hari ta sama, inda suka lalata 2 daga cikin 4 na bindigogin nasu da kuma dukkan ’yan ta’addan da ke dauke da makamai.

Kakakin ya kuma ce akwai alamun cewa wani babban Kwamandan ’yan ta’addan da ake cewa Abu Asad, jigo a kungiyar Ali Ngulde a karkashin Boko Haram, da mayakansa da dama na daga cikin ’yan ta’adda da aka kashe  a harin ta sama.

Ya ce Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya yaba wa kwamandan rundunar da sojojin sama, yayin da ya bukace su da su ci gaba da hadin gwiwa da na kasa yayin da suke ci gaba da kai hare-hare, ta yadda ’yan ta’addan za su ci gaba da guduwa da kafafunsu.