Sojoji sun kashe ’yan bindiga 12, sun kwato makamai a Zamfara

Sojojin sun samu nasarar ne bayan kai wasu hare-hare a jihar.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 12, sun kwato makamai a Zamfara

Dakarun Rundunar Operation Hadarin Daji, sun kashe ’yan bindiga 12, tare da kwato makamai da shanu 18 a Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar, Laftanar Suleman Omale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau a ranar Asabar.

Omale, ya ce nasarar da dakarun suka samu ta biyo bayan kai hare-hare da rundunar sojin Najeriya ke yi da nufin tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

Ya ce dakarun sun mamaye yankunan Babban Doka, Gobirawar Challi da Kabaro da ke Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

“A yayin samamen sojojinmu daga yankin Dansadau sun nuna ƙwarewa, inda suka hallaka ’yan ta’adda 12, wasu kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.

“A yayin artabun an ƙwato manyan makamai ciki har da bindiga AK-47 guda ɗaya da harsasai.

“Bugu da ƙari, sojojin sun kuma ƙwato shanu 18, babura 10 daga hannun ’yan ta’addan tare da lalata maɓoyarsu,” in ji shi.

Omale ya ce Kwamandan rundunar, Birigediya Janar Sani Ahmed, ya yaba wa sojojin kan ƙoƙarin da suke yi.

“Dakarun su ci gaba da kai ire-iren waɗannan hare-haren domin kawo ƙarshen ‘yan ta’adda,” in ji Ahmed.

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe