Sojoji sun kashe `yan bindiga 23 da kwato mutum 40 a Zamfara
Rundunar sojojin Najeriya na Operation Sharan Daji da ke jihar Zamfara sun yi nasarar kashe `yan bindiga 23 da kama 18 wandanda ake zargin masu kaiwa `yan garkuwan mutane bayanai ne da barayin shanu kuma suke yi masu safarar makamai a jihar. Mukaddashin jami’in sadarwa na rundunar Operation Sharan Daji, Manjo Clement Abiade, ne ya […]
Rundunar sojojin Najeriya na Operation Sharan Daji da ke jihar Zamfara sun yi nasarar kashe `yan bindiga 23 da kama 18 wandanda ake zargin masu kaiwa `yan garkuwan mutane bayanai ne da barayin shanu kuma suke yi masu safarar makamai a jihar.
Mukaddashin jami’in sadarwa na rundunar Operation Sharan Daji, Manjo Clement Abiade, ne ya fitar da sanarwar, ya kuma ce dakarun `operation SHARAN DAJI` da ke yaki a jirajen sama sun kai samame a unguwannin Kagara, Gando, Fankama, Fete da dajin Dumburum.
Manjo Clement, ya ce dakarun su sun yi nasarar kama wani shahararren mai garkuwa da mutane mai suna Muhammed Iso, da hadin gwiwar jami’an tsaron jamhoriyar Nijar.