Sojoji sun kashe `yan bindiga 25 a Zamfara

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta  na ‘Operation Diran Mikiya’ sun tarwatsa sansanin ‘yan bindigar na unguwar Ajia yayin da suka kashe akalla 25 a  Ajia da Wonaka a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara. Kakakin rundunar sojojin saman Iya Kwamando Ibikunle Daramola, ya ce dakarunsu sun fara kaiwa ‘yan bindigar […]

Sojoji sun kashe `yan bindiga 25 a Zamfara

Jirgin sojojin saman Najeriya. (Hoto: nileinternational.net)

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta  na ‘Operation Diran Mikiya’ sun tarwatsa sansanin ‘yan bindigar na unguwar Ajia yayin da suka kashe akalla 25 a  Ajia da Wonaka a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojojin saman Iya Kwamando Ibikunle Daramola, ya ce dakarunsu sun fara kaiwa ‘yan bindigar farmaki ne a ranar 4 ga Afrilu 2019 ta hanyar bin matakan sirri, sojojin sun bankado cewa, maharan na amfani da wasu wurare a unguwar Ajia a matsayin maboya makaman su.