Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3, sun kama 6 a Kaduna

Sojojin sun kama wasu daga cikin ’yan bindigar bayan samun bayanan sirri.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3, sun kama 6 a Kaduna

Sojoji sun harbe ’yan bindiga uku tare da kama wasu shida a kauyen Kohoto da ke kusa da Janjala a Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Wani mazaunin Janjala, Abdullahi Zayyanu, ya ce harbin tare da kame wadanda ake zargin ya biyo bayan kama shugabansu, Mu’azu Baushe a Kagarko a makon jiya.

Ya bayyana cewa, “Mu’azu, wanda ake kira da Baushe, ya je kasuwar Kagarko a makon da ya gabata domin saya wa mutanensa kayan abinci da kayan shaye-shaye, aka sanar da sojoji, suka je suka kama shi.”

’Yan bindiga dai sun addabi al’ummar yankunan Akoti, Gundiri, Taka-Lafiya, Sadauna, Dutse da Janjala a Karamar Hukumar Kagarko.

Sai dai babu wani martani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna kan wannan cigaban.

Yanzu Yanzu: Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Kano, Haruna Zago ya rasu

NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa

Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025

Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda