Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 3, sun kwato makamai a Taraba

Dakarun sun jadadda aniyar ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a jihar.

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 3, sun kwato makamai a Taraba

Dakarun Sojin Runduna ta 6, sun yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga uku a Karamar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Laftanar Olabodunde Oni, jami’in hulda da jama’a na rundunar, a Jalingo a ranar Alhamis.

Ya ce sojojin sun samu nasarar kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu, babur guda daya da kuma harsasai.

A cewarsa, dakarun sun kai farmakin ne a garin Chibi, bayan samun bayanan sirri, inda suka yi wa maharan dirar mikiya.

Kazalika, ya ce dakarun na ci gaba da aiki tukuru don wanzar da zaman lafiya da tsaro a Taraba.

Sanarwar ta kuma ce, Kwamandan rundunar ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa dakarun kan jajircewa da kuma kwazo wajen aiwatar da aikin.

Oni ya kuma ce, Kwamandan ya jaddada aniyar rundunar na kawar da masu aikata laifuka a jihar tare da tabbatar da tsaro ga al’ummar jihar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja