Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina

Dakarun soji na ci gaba da ƙaimi a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’adda a jihar.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 31 tare da lalata sansaninsu a Jihar Katsina, yayin wasu hare-hare guda biyu da suka kai.

A farmaki na farko, dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da ’yan bindiga a garin Maigora da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.

Da farko, sojojin sun kashe ’yan bindiga biyar bayan sun kai farmaki garin.

Sai dai lokacin da suka sake haɗuwa don kai harin ramuwar gayya, sojojin sun sake kashe guda bakwai, ciki har da Dogo, wanda babban Kwamanda ne a cikinsu.

Haka kuma, sojojin sun ƙwace babura guda bakwai da ‘yan bindigar ke amfani da su.

A wani farmakin, rundunar sojojin sama ta yi luguden wuta a maboyar ’yan bindiga da ke dajin Unguwar Goga, Ruwan Godiya, a Ƙaramar Hukumar Faskari.

Sun lalata sansanin shugabannin ’yan bindiga biyu; Alhaji Gero da Alhaji Riga, inda suka kashe aƙalla mahara 19.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin Najeriya na ƙara ƙaimi wajen murƙushe ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, tare da lalata sansaninsu.

Har ila yau, sojojin na ci gaba da sintiri ta sama da ƙasa don daƙile yunƙurin ’yan bindiga na sake hare-hare.