Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 sun ceto mutane 20 a Kaduna

Sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 da sauran makamai da baburan ’yan fashin dajin

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 sun ceto mutane 20 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan bindiga huɗu sannan suka ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi da ke Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce a yayin wani samame a yankin Alawa da ke Birnin Gwari, sojojin suka fatattaki ’yan bindiga a Dajin Kwaga.

Ya ƙara da cewa sojojin sun kashe biyu a cikin ’yan bindigar sannan suka ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da sauran makamai da baburan ’yan fashin dajin.

A wani samame na daban a yankin Nakwakina da ke Giwa kuma, sojoji suka yi wa ’yan bindiga kwanton ɓauna.

A nan kuma “suka kashe biyu daga cikin ’yan bindigar, sauransu kuma suka tsere da raunukan harbi,” in ji Aruwan.

Ya ce a nan ma sojojin sun ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da wasu makaman da babura.