Sojoji sun kashe ’yan bindiga, sun kama wasu 19 a Filato da Kaduna
Sojojin sun samu nasarar ne bayan samun wasu bayanan sirri.
Dakarun da ke aiki da rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’ (OPSH) sun kashe ’yan bindiga hudu tare da cafke akalla wasu 19 da suka hada da masu garkuwa da mutane da barayin shanu a wani samame da suka kai maboyar ’yan ta’adda a Jihohin Filato da Kaduna.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne a shafinta na X (Twitter) a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwamba, 2023.
- ’Yan bindiga sun yi wa masu taron Mauludi yankan rago a Katsina
- Afirka ta Kudu ta janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Isra’ila
Sanarwar ta ce, “An kama mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. An kama uku da laifin yin garkuwa da mutane yayin da hudu aka kama su da laifin kisan kai.
“An kama mutum hudu da ake zargi da kai hare-hare a kauyuka, biyu kuma da laifin safarar miyagun kwayoyi, yayin da aka kashe ’yan bindiga hudu.
“Har ila yau, an ceto mutum hudu daga hannun ’yan bindiga, yayin da aka dakile hare-hare shida,” in ji sanarwar.
A ranar 29 ga watan Oktoba, 2023, sojojin sun ce sun kama wasu da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, inda suka kwato bindigogi a hannunsu.
Sanarwar ta kuma ce kashegari jami’an OPSH na sashe na 7 sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne a kauyen Kamuru da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar Kaduna tare da kwato bindiga daya da harsasai a hannunsa.
“A ranar 30 ga watan Oktoba, 2023, bisa ga sahihin bayanai sojoji sun kama wasu mutum uku, kan harin da aka kai wa manoma a kauyen Mai Hakorin Gwal da ke karamar hukumar Bokkos, a jihar Filato.
“Kazalika, sojoji sun kama wasu mutum uku dangane da kisan wani dan kasuwa mai suna Abdulkarim Saidu, a kauyen Shonong da ke karamar hukumar Riyom, jihar Filato.
“An kama wadanda ake zargin ne a kauyen Fang da ke karamar hukumar Riyom a ranar 30 ga watan Oktoba 2023,” in ji sanarwar.
A ranar 1 ga watan Nuwamba, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar babura a yankin Riyom na jihar Filato.
Sojojin tare da hadin gwiwar rundunar CJTF sun kuma ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a unguwar Zobolo da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Sun kama wani mutum a ranar Juma’a, 3 ga watan Nuwamba a kauyen Gidan Auta bisa laifin yin garkuwa da mutum biyu da aikata fyade a ranar 24 ga watan Satumba.
A ranar ne jami’an tsaro da ke sashe na 4 na rundunar OPSH suka kama wani dan fashi da makami a kauyen Kwog da ke karamar hukumar Barkin Ladi.
Wanda aka kama na daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo bisa wasu ayyukan fashi da makami a Barkin Ladi.
Kwamandan Operation SAFE HAVEN, Manjo Janar AE Abubakar, ya jaddada jajircewar rundunar yayin da ya bukaci al’ummar jihar Filato da Kaduna da Bauchi su ci gaba da tallafa wa sojojin.
Ya kara da cewa za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a kotu bayan kammala bincike.