Sojoji sun kashe ’yan bindigar Zamfara 58

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ’yan bindigar Zamfara 58 a karkashin  shirinta na ‘Operation Sharar Daji’ don yakar barayin shanu da  masu garkuwa da mutane da suka addabi Jihar Zamfara. Sojojin sun kashe ’yan bindigar ne a dajin Dumburum da Gando ranar Lahadi da ta gabata, kamar yadda Mukaddashin Kakakin Rundunar, Manjo Clement Abiade ya […]

Sojoji sun kashe ’yan bindigar Zamfara 58

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ’yan bindigar Zamfara 58 a karkashin  shirinta na ‘Operation Sharar Daji’ don yakar barayin shanu da  masu garkuwa da mutane da suka addabi Jihar Zamfara. Sojojin sun kashe ’yan bindigar ne a dajin Dumburum da Gando ranar Lahadi da ta gabata, kamar yadda Mukaddashin Kakakin Rundunar, Manjo Clement Abiade ya sanar a shekaranjiya Laraba.

Ya ce sojojin sun kama daya daga cikin ’yan bindigar da ransa, sun kuma tarwatsa sansanonin ’yan bindigar guda 18 yayin da suka kubutar da mutum 75 da aka yi garkuwa da su a wasu daga cikin sansanonin. Mafi yawan wadanda aka kubutar mazauna wasu kauyukan Jihar Zamfara ne, kuma bayan kubutar da su sun koma wurin iyalansu.

Wasu daga cikin makaman da sojojin suka kwato sun hada da, manyan bindigogi 5 da bindigogi 4 kirar AK47 da bindigogi kirar gida 10 da karamar bindiga kirar pistol 1 da kuma babura 40.

Wannan shirin na ‘Operation Sharar Daji’ ya fuskanci kalubale wanda hakan ya sa, suka rasa sojoji biyu da wasu jami’an bijilanti biyu.

“An samu adadin sojoji 8 da ’yan bijilanti 6 da suka samu mummunan rauni sanadiyyar harbin bindiga. An dai kai wadanda suka samu raunukan Cibiyar Lafiya ta Tarayya ta Gusau, don yi musu jinya, yayin da wadanda suke cikin mawuyacin hali, aka kai su asibiti na musamman don lura da lafiyarsu cikin gaggawa.

“An sanar da iyalan sojojin da suka rasu yayin da ’yan bijilantin da suka rasu aka binne su a makabartar Anka, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” inji shi.

Abiade ya ce an kaddamar da shirin ‘Operation Sharar Daji’ don dakile kisan gillar da ’yan bindigar ke yi wa jama’a a jihohin Zamfara da Katsina a watan Janairun bana, wanda zai kai har zuwa watan Yuni. Ya ce shirin an kaddamar da shi ne ta hadin gwiwar hukumomin tsaro da ’yan bijilanti.

Kwamandan Operation Sharar Daji, Manjo Janar S.O. Olabanji ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu don kare martabar kasarsu.

Ya tabbatar da kokarin jami’an Operation Sharar Daji na dakile duk wani shiri na ’yan bindiga da ’yan fashi da makami da sauran masu aikata laifuffuka a Jihar Zamfara. Don haka ya bukaci jama’ar jihar su bai wa sojojin hadin kai wajen samar musu da bayanai a kan barayin a duk inda suke, don dakile shirinsu.

 

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta