Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Mayaƙan Boko Haram 30 sun sheka lahira bayan da sojoji suka ragargaje su a yankin Kareto da ke Jihar Borno

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Sojojin Nijeriya sun halaka mayaƙan Boko Haram 30 a yayin artabu da mayaƙan Boko Haram da suka kai musu hari a Jihar Borno.

Kakakin Rundunar Tsaro ta Nijeriya, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojojin sun aika mayaƙan na Boko Haram lahira tare da ƙwato malamansu ne a yankin Gubio, inda dakarun ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Sai dai ya ce an yi rashin sa’a mutum biyar daga cikin sojoji sun kwanta dama, wasu 10 sun samu raunuka a yayin da ake ci gaba da neman wasu huɗu da ba a gani ba bayan musayar wutar.

Ya ce bayan matakan sun kai wa sojojin hari suka lalata wasu kayan yaƙinsu ne jirgin yaƙi ya kai wa dakarun ɗauki ya ragargaza maharan.

Wata majiyar tsaro ta ce mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojojin hare-hare ta ɓangarori daban-daban ne da nufin ƙwace sansanin soja na dakaru na musamman da ke Gubio.

Majiyar ta ce, “a ranar 16 ga watan Nuwambar nan mayaƙan Boko Haram/ISWAP sun kai hari suka kashe soja 18 suka jikkata wasu da dama, su kuma aka kashe musu mutum shida.

“A wannan harin kuma an kashe sojoji biyar, amma sojojin suka aika ’yan ta’adda 30 lahira.”

A baya-bayan nan ne sojoji suka fara aikin samar da tsaro a yankin Kareto da ke Karamar Hukumar Gubio da nufin bayar da kariya ga ’yan gudun hijirar yankin da ake shirin mayarwa gidajensu.

Hakan kuwa na zuwa ne a yayin ayyukan Boko Haram da ISWAP ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, duk kuwa da ƙoƙarin rundunar haɗin gwiwar ƙasashe Chadi da Nijar da Najeriya da ke ƙoƙarin murƙushe ’yan ta’addan.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya