Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 8 a Baga
Rundunar sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram takwas a wani sabon farmaki da suka kaiwa ‘yan kungiyar a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno. Mataimakin Daraktan hulda jama’a na rundunar sojojin Najeriya Kanal Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a Maiduguri, kuma sun kwato makamai da yawa daga hannun ‘yan […]
Rundunar sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram takwas a wani sabon farmaki da suka kaiwa ‘yan kungiyar a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Mataimakin Daraktan hulda jama’a na rundunar sojojin Najeriya Kanal Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a Maiduguri, kuma sun kwato makamai da yawa daga hannun ‘yan kungiyar.