Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram masu shigar mata
Umarnin da Hafsan Hafsoshin Sojin kasa Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayar cewa sojoji su rika kai hari ga mayakan Boko Haram, maimakon su jira su farmake su ya fara haifar da da mai ido, inda sojojin suka hallaka ’yan Boko Haram da dama a hanyar Dikwa zuwa Maiduguri da ke Jihar Borno. Sojojin […]
Umarnin da Hafsan Hafsoshin Sojin kasa Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayar cewa sojoji su rika kai hari ga mayakan Boko Haram, maimakon su jira su farmake su ya fara haifar da da mai ido, inda sojojin suka hallaka ’yan Boko Haram da dama a hanyar Dikwa zuwa Maiduguri da ke Jihar Borno.
Sojojin sun kuma hallaka ’yan Boko Haram masu shigar mata a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a yammacin Lahadin da ta gabata, inda wani namiji da ya yi cikakkiyar shigar mata ya sha wuta a hannun sojojin Najeriya da ke aiki a karkashin shirin Zaman Lafiya Dole tare da wani dan ta’adda da ke tuka shi a mota. An gano kayan hada bama-bamai da kan bindigar harbor jiragen sama a cikin jakarsa ta mata.
Lokacin da Janar Buratai ke kaddamar da Shirin Zaman Lafiya Dole “Operaton Zaman Lafiya Dole,” ya umarci sojoji su daina jira sai ’yan Boko Haram sun kawo musu hari maimakon haka su rika kai musu hari har maboyarsu. Kuma a cewar wata majiya ta tsaro wannan ne ya sa sojojin suka kara azamar kai hari inda hakan ya yi sanadin kashe ’yan ta’adda da dama.
Hare-harenn hadin gwiwa da ya hada sojin sama da na kasa sun yi ritsa da ’yan ta’addan kuma an kwato bama-bamai da babura da wata babbar mota dauke da bindigogin kakkabo jiragen sama da bindiga mai sarrafa kanta da harasasai da bindigogi da dama.
Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka wanda ya ki bayar da adadin mutanen da suka hallaka a hare-haren ya tabbatar da kaddamar da harin a kan ’yan ta’addan. Ya ce yunkurin na baya ya jawo karbo hanyoyin da Boko Haram suke iko da su tare da lalata bama-baman da suka daddasa a hanyar Biu zuwa Buni Yadi zuwa Damaturu da Biu zuwa Sabon Gari zuwa Damboa.
Sojojin sun kuma karbo garin Dikwa a Jihar Borno daga hannun Boko Haram, bayan sun kashe ’ya’yanta 20 tare da lalata sansanoninsu da karbe miyagun makamai da motoci kirar a-kori-kura biyar.
Kakakin Rundunar Soji ta Bakwai da ke Maiduguri, Kanar Tukur Gusau, ya shaida wa manema labarai, cewa a yanzu babu wata karamar hukuma da take hannun ’yan Boko Haram, sun koma lunguna da kauyuka da dazuka suna fitowa su yi kisa su koma, kuma in Allah Ya so soji za su kakkabe su.