Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram Sun Ceto Mata 3

Dakarun kasar Nijar a yankunan Gagam da Tchantchandi sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama sannan suka ceto wasu mata da aka yi garkuwa da su

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram Sun Ceto Mata 3

Makaman da sojoji suka kwato bayan hallaka mayakan Boko Haram.

Dakarun kasar Nijar da aka tura yankunan Gagam da Tchantchandi sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani Gumurzun a tsakaninsu.

Sojojin, karkashin rundunar haɗin gwiwa ta Multi National Joint Task Force (MNJTF) sun kuma yi nasarar ceto wasu mata daga hannun mayaƙan ƙungiyar da suka yi garkuwa da su.

Sojojin sun ragargaji ’yan ta’addan ne a ranar 27 ga watan Nuwamba l a yankin Ouhou na kasar Nijar, a matsayin martani ga sace wasu mata biyu da Boko Haram ta yi yankunan Dagaya da Tchantchandi.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, ’yan ta’addan suna ƙoƙarin tserewa ne sojojin Nijar da na Chadi suka yi gaggawar kutsawa cikinsu suka kashe da dama daga cikinsu, suka kubutar da matan da aka yi garkuwa da su.

Sojojin sun kuma kwato bindigogi ƙirar AK-47 daga hannun ’yan ta ’addan.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024