Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram uku sun kama daya a Gombe

A ranar Lahadin da ta gabata ne sojoji a Jihar Gombe suka samu nasarar bindige wasu ’yan Boko Haram uku a dajin Dukku inda suka kama daya da ransa. Da yake gabatar da gawarwaki da kayan da suka samu daga wurin ’yan Boko Haram din, kakakin bataliyar soji ta 301 da ke Gombe, da ya […]

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram uku sun kama daya a Gombe
Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram uku sun kama daya a Gombe

A ranar Lahadin da ta gabata ne sojoji a Jihar Gombe suka samu nasarar bindige wasu ’yan Boko Haram uku a dajin Dukku inda suka kama daya da ransa.

Da yake gabatar da gawarwaki da kayan da suka samu daga wurin ’yan Boko Haram din, kakakin bataliyar soji ta 301 da ke Gombe, da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce sun samu nasarar ce a lokacin da suka yi ba-ta-kashi da mayakan Boko Haram din.
Ya ce sun kwato kayayyaki a wurin mayakan Boko Haram din da suka hada da mota kirar Hilud da na’urar tantance katin zabe na Hukumar INEC da akwatuna uku da alburusai da bindiga daya kirar FM da yunifom na ’yan sanda da sauran kayayyaki.
Ya ce sun fafata ne a daren Lahadi wayewar garin Litinin a lokacin da ’yan Boko Haram din suka yi kokarin kai hari a wani shingen bincike ababen hawa na soji da ke karamar Hukumar Dukku.
Jami’in ya roki jama’a su zauna cikin lumana, inda ya ce a shirye suke su kare rayuka da dukiyoyin al’umma a sassan jihar da kasa baki daya.
“Mun gode wa daukacin al’ummar garin Dukku da Jihar Gombe kan hadin kan da suke ba mu, idan muka ci gaba da samun hadin kansu za mu iya kawar da duk wani batagari ko gungun miyagu masu neman tada kayar baya,” inji shi.
Idan za a iya tunawa a ranar Asabar da ta gabata wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kashe wasu mutane da dan majalisar Jihar Gombe mai wakiltar mazabar Dukku ta Kudu Alhaji Umar Aminu da ake kira da Mai Masallaci, suka kuma lalata wasu kayayyaki na hukumar zabe.
Daga baya al’amura sun daidaita inda aka yi zabe babu wani tashin hankali a yankin.