Sojoji sun kashe ‘yan fashi 58 da kubutar da mutum 75 a Zamfara

A shirin da sojoji suke yi na ‘Operation Sharan Daji’ a jihar Zamfara sun kashe ‘yan fashi da makami 58 a dajin Dumburum da Gando a ranar Lahadin da ta gabata. Jami’in sadarwa na shirin Operation Sharan Daji Manjo Clement K Abiade, ne ya sanar da hakan. Sojojin dai nata kai samame ne don dakile […]

Sojoji sun kashe ‘yan fashi 58 da kubutar da mutum 75 a Zamfara

A shirin da sojoji suke yi na ‘Operation Sharan Daji’ a jihar Zamfara sun kashe ‘yan fashi da makami 58 a dajin Dumburum da Gando a ranar Lahadin da ta gabata.

Jami’in sadarwa na shirin Operation Sharan Daji Manjo Clement K Abiade, ne ya sanar da hakan.

Sojojin dai nata kai samame ne don dakile harin ‘yan fashi da makami da kuma barayin shanu da suka addabi yankunan karkara a jihar.

Sojojin sun yi nasarar lalata sansanonin ‘yan fashin guda 18 tare da sako mutum 75 da aka yi garkuwa da su, kuma a yanzu sun koma wurin iyalansu.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta