Sojoji Sun Kashe ’Yan ISWAP Sun Kwato Matafiya Da Aka Sace A Yobe
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP hudu tare da kubutar da wasu fasinjoji da kungiyar ta yi garkuwa da su a Buni Yadi, Jihar Yobe.
Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP hudu tare da kubutar da wasu fasinjoji da kungiyar ta yi garkuwa da su a Buni Yadi da ke Jihar Yobe.
Wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ruwaito majiyoyin sirri da suka tabbatar da cewa arangamar ta faru ne a kauyen Lamisuri da ke cikin Karamar Hukumar Gujba.
A safiyar ranar Juma’a ’yan ta’adda a kan babura suka tare wasu motocin haya a hanyar zuwa Kwalejin Aikin Gona ta Jihar Yobe da ke kusa da Buni Yadi, inda suka yi awon gaba da fasinjojin zuwa cikin daji.
Rundunar sojin ta ce, jin rahoton hakan ne nan take ta aika da dakarunta da ke sintiri suka bi sawun ’yan ta’addar zuwa cikin dajin.
Majiyar ta kara da cewar, ba a jima ba sojojin suka yi nasarar gano daya daga cikin motocin da aka yi awon gaba da su, wadda ke dauke da mata da yara zuwa garin Biu da ke Jihar Borno.
Wannan gumurzu da sojojin suka yi da wadannan ’yan ta’addan ne ya kai ga kwato fasinjojin da aka yi garkuwa da su.