Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 1,160 sun ceto mutane 721
An kama ’yan ta’adda 1,096 tare da a watan Agusta, 2024, a cewar Hedikwatar Tsaro ta Najeriya
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojojin kasar sun kashe ’yan ta’adda 1,166 tare da kama wasu 1,096 da ransu a cikin watan Agustan nan da ke bankwana.
Rundunar tsaron ta ce, a yayin wannan aiki, sojojin sun ƙwato mutane 721 da ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da su.
Daraktan Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaro, Birgediya-Janar Edward Buba, ya bayyana cewa sojojin sun kuma hallaka wasu jagororin Boko Haram da ISWAP da na ’yan bindiga a yayin aikin.
Edward Buba ya shaida wa ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis cewa, kwamandojin ISWAP da Boko Haram ɗin da sojoji suka kashe a Arewa maso Gabas sun haɗa da Munir Arika, Sani Dilla (Ɗan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, Bakoura Araina Chikin, Dungusu, Abu Darda da kuma Abu Rijab.
- Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan fashin daji 37 a Zamfara
- Gwamnati ta bai wa ’yan kasuwa wata guda su karya farashin kaya
Jagororin ’yan bindigar Arewa maso Yamma da aka kashe kuma su ne; Kachalla Dan Ali Garin Fadama, Kachalla Dan Mani Na Inna, Kachalla Basiru Zakariyya, Sani Baka Tsine, Inusa Zangon Kuzi, Ibrahim, Tukur da kima Kamilu Buzaru.
Ya ce “sojojin sun kawo bindigogi 391 da harsasai 15,234 sannan sun daƙile yunƙurin satar ɗanyen mai da jimillar kuɗinsa ya kai Naira biliyan biyar.
“Bindigogin da aka ƙwato a watan na Agusta sun haɗa da AK-47 guda 208, ƙirar gida 54, harbi-ruga 53, pump action 36 da kuma harsasai nau’i daban-daban guda 15,234.
“Sai ɗanyen man sata lita 5,047,150, da lita 1,152,500 na dizel da aka tace ba bisa ka’ida ba, lita 320 na kananzir irinsa da kuma fetur lita 28,500 da sauransu.”
A cewarsa, kusan a kullum mayaƙan Boko Haram da ISWAP suna miƙa wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas, sakamakon ƙara murƙushe su da sojojin ke yi a can.
Ya ce sojojin ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da samuwar tsaro da kuma murƙushe manya da ƙananan ’yan ta’addan da sauran nau’ikan barazanar tsaro.