Sojoji sun bindige ’yan ta’adda 3 a Zamfara
Sojoji sun bindige ’yan ta’addan har lahira a yayin musayar wuta a ƙananan hukumomin Ƙaura Namoda da Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara
’Yan ta’adda uku sun sheƙa lahira bayan sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma sun yi musu luguden wuta ƙananan hukumomin Ƙaura Namoda da Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar, Laftanar-Kanar Aliyu Danja, ya ce sojojin suna ci gaba da samun nasarori wajen yaƙar ’yan ta’adda da sauran miyagu a jihar Zamfara, a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.
“Da safiyar Alhamis, 7 ga Mayu, 2026, ne sojojin Operation Fansan Yamma suka shiga sintiri a Ƙaura Namoda da Birnin Magaji da nufin hana ’yan ta’adda yin tasiri a yankin, in ji shi.
Ya bayyana cewa a lokacin aikin, sojojin sun yi arangama da ’yan ta’adda a ƙauyen Dumburum, inda aka yi musayar wuta mai tsanani.
- Bom ya kashe mutane 6, ya jikkata 7 a Zamfara
- Sojoji sun gano masana’antun ƙera haramta makamai a Filato
Ya ce sojojin sun yi nasara da ƙarfin makamai, suka tilasta ’yan ta’addan tserewa bayan sun yi asarar rayuka.
Ya bayyana cewa sojojin sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da ƙwace makamai da harsasai da suka haɗa da bindiga AK-47 guda ɗaya, mashin-gun guda daya, bindiga da aka ƙera a gida guda daya, da harsasai 571.
“Abu mai muhimmanci shi ne babu wani soja da ya jikkata a yayin aikin,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa nasarorin da rundunar take samu hujja ce ta jajircewa, ƙwarewa da ƙwazon sojojin wajen yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar samar da bayanai na gaskiya a kan lokaci kan ayyukan ‘yan ta’adda domin ƙara inganta ayyukan tsaro da nufin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Zamfara da Arewa maso Yamma baki ɗaya.