Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ceto Mutum 22 A Borno
Dakarun sun kuma jikkata wasu daga cikin mayaƙan na Boko Haram.
Dakarun Sojin Najeriya sun samu nasarar kashe ƙarin wasu ’yan ta’addan Boko Haram guda uku a wani samame da suka kai ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno.
Sun kai harin ne a ranar 13 ga watan Yuli, 2024, inda suka kashe ’yan ta’addan, yayin da wasu tsere da raunin biniga.
- Gwamnan Gombe ya gana da Tinubu kan aikin Kolmani
- Abin da ya ja hankalina na musulunta — Rabaran Adamu Shani
Wani masani kan harkar tada ƙayar baya, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun ceto mutum 22 tare da lalata wasu gine-ginen da ke taimaka wa ’yan ta’addan wajen gudanar da ayyukansu na ta’addanci.
Nasarar dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 48, inda suka kashe mayaƙan Haram shida tare da ceto wasu mutum 57 daga sansanin ’yan ta’addan.
Dakarun sun kuma kora da dama daga mayaƙan na Boko Haram zuwa daji ɗauke da raunukan harbin bindiga.