Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 30 a kusa da tafkin Chadi

Hare-haren sun lalata kwale-kwalen tare da tarwatsa hanyoyin samar da kayan aikin ’yan ta’addan.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 30 a kusa da tafkin Chadi

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas karkashin Operation HADIN KAI, sun kashe akalla ’yan ta’adda 30 a kusa da Tafkin Chadi a Jihar Borno.

An gudanar da wannan farmaki ne daga daren ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba a yankin tibirin Kaniram.

Mai magana da yawun Operation HADIN KAI, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce sojojin sun kuma lalata wasu kwale-kwale da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen zirga-zirga da kai kayan aiki.

Ya bayyana cewa jiragen yakin sojoji sun dade suna sa ido a yankin, inda suka gano sama da kwale-kwale 30 na ’yan ta’adda.

A cewarsa, dakarun sun dauki mataki ne bayan samun sahihan bayanan sirri, sannan suka kai hare-hare ta sama bayan tabbatar da wuraren da maharan suke.

Hare-haren sun lalata kwale-kwalen tare da tarwatsa hanyoyin samar da kayan aikin ’yan ta’addan.

Uba, ya ce an kuma kai wa ’yan ta’addan karin hare-hare bayan sun yi kokarin tserewa zuwa cikin dazuka, lamarin da ya yi sanadin kashe sama da mayaka 30.

Ya kara da cewa wannan farmaki ya raunana ’yan ta’addan sosai ta hanyar rage musu karfi.