Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 16

Dakarun sun jaddada aniyarsu na ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin Najeriya.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 16

Dakarun Sojin Najeriya, sun kashe ’yan ta’adda takwas tare da ceto wasu mutum 16 da aka yi garkuwa da a wani samame da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Yayin samamen sun yi nasarar ƙwato bindigogi da wasu kayayyaki, a ƙoƙarinsu na yaƙi da ta’addanci.

A ranar 22 ga watan Satumba, sojoji a Jihar Borno, sun daƙile harin ’yan ta’adda a wasu ƙauyuka, inda suka kashe uku daga cikin maharan tare da ƙwato makamai ciki har da bindiga ƙirar AK-47.

A wani samame da suka kai ƙaramar hukumar Gwoza, sojojin sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su, ciki har da maza 10 da mata shida, sai dai sun kashe ɗan ta’adda guda ɗaya.

A Jihar Yobe kuwa, sojojin sun kai wa ’yan ta’adda hari inda suka kashe huɗu daga cikinsu, a ƙauyukan Madza da Azare bisa bayanan sirri da suka samu.

Sun kuma ƙara ƙwato wasu makamai a yayin wannan samame.

Kazalika, sojoji a Abuja sun kama wani mutum ɗauke alburusai da aka ɓoye a cikin buhun gari.

Rundunar Sojin Najeriya ta sake tabbatar da aniyarta na kawo ƙarshen ta’addanci, tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da samar da bayanai da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen yin aikinsu cikin inganci.