Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 40 a jihohi 4

Dakarun sun kai samamen ne a lokuta mabanbanta.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 40 a jihohi 4

Dakarun Sojin Najeriya, sun kashe ’yan ta’adda takwas tare da ceto wasu mutum 40 a wasu samame da suka kai a jihohin Nasarawa, Borno, Kaduna, da kuma Yobe.

Rundunar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na sada zumunta, inda ta bayyana nasarorin da ta samu.

A yayin hare-haren da ta kai, sojojin sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mai safarar makamai, sannan sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

A Jihar Nasarawa, sojojin sun kama wani mai safarar makamai ɗauke da harsasai 303 a lokacin da suka gudanar da bincike a kan hanyar Lafia zuwa Keffi.

A Jihar Kaduna kuwa, sojojin sun kai hari dazuka, inda suka kashe ’yan ta’adda uku, suka kuma ƙwace makamai da babura.

A Jihar Borno, sojoji sun samu nasarar ƙwace bindigogi da harsasai bayan wani gumurzu da suka yi da ‘yan ta’adda.

Kazalika, sojoji sun kama motoci ɗauke da kayayyakin abinci da ake zargin ’yan ta’adda za a kai wa.

Sannan sun ceto mutum 38 da suka haɗa da maza, mata, da yara, waɗanda ‘yan ta’addan ke kokarin sauyawa matsuguni.

A Jihar Yobe kusa, sojoji sun yi kwanton-ɓauna a ƙauyen Sasawa, inda suka kashe ɗan ta’adda ɗaya, suka ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da babur guda ɗaya.

Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike da sauran hare-hare domin kamo sauran masu laifi da kuma tabbatar da zaman lafiya a waɗannan yankuna.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra