Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 80, wasu 876 Sun Mika Wuya A Borno

Yadda sojoji suka ragargaji mayakan ISWAP da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 80, wasu 876 Sun Mika Wuya A Borno

Wasu mutane da sojoji suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram/ISWAA a Jihar a Borno

Dakarun soji da ke yakar ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe  mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP guda 80, a yayin da wasu 876 suka mika wuya a makonni biyun da suka gabata.

Kakakin rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya ce sojojin hadin gwiwa da ke Tafkin Chadi (MNJTF) sun kashe kwamandoji da mayakan kungiyar ISWAP 55 a yankin Arege da ke Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno.

“Sojoji sun kuma kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 25, suka kwato bindigogi 30 da sundukan albarusan AK-47 guda 12 da gurneti daya da sauran makamai.

“Jimillar mayaka da iyansu 876 kuma — wadanda suka hada da manya maza 89 da mata 249 da kananan yara 538 — sun mika wuya ga sosoji a wurare daban-daban,” in ji shi.

Wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana a Maiduguri cewa, sojojin sun lalata motoci 13 da babura da na’urorin tayar da abubuwan fashewa guda biyar mallakin kungiyoyin.

Manjo-Janar Danmadami ya kara da cewa an kashe kwamandojin kungiyar da dama a wani samame na kwanaki 22 wanda ya kare a ranar 28 ga Mayu, 2023 a yankin Harbin Zuma da ke Gabar Tafkin Chadi.

Ya ci gaba da cewa “Daga 18 ga watan Mayu zuwa 1 ga Yuni, 2023 sojoji suka kai wani samamen domin fatattakar ’yan ta’dda daga sansanoninsu da aka gano a kauyuka da dazuzzuka da tsaunukan Konduga da Abadam.

“Sauran wuraren su ne Guzamala da Ngala da Bama da Dikwa da Gubio da Damboa da Jere da Kukawa da kuma Magumeri.”

Ya shaida wa mahalarta wani taron kara wa juna sani kan ayyukan sojoji da nasarorin da suka samu, wanda rundunar ta shirya a hedikwatarta da ke Maiduguri cewa, wannan nasara ce a kokarin sojoji na murkushe ’yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a yankin Arewa maso Gabas.

Ma’aikatar Tsaro ta kasar Jamhuriyar Nijar ta ce an kai wani hari a kan mayakan ISWAP da kwamandojinsu da ke yankin Tumbums Triangle.

Wata majiyar soji a Maiduguri ta ce kwamandojin da aka kashe sun hada da Fiya Abouzeid da Qaid Malam Moustapha, da kuma wasu malamai da ba a bayyana sunayensu ba.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja