Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 99, sun kuɓutar da mutum 139 a mako guda

An gudanar da ayyukan ne a fadin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 99, sun kuɓutar da mutum 139 a mako guda

Dakarun sojin Najeriya masu yaki da ta’addanci sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 99 tare da kame wasu 198 a wani samame da suka shafe mako guda ana yi.

Daraktan yada labarai na Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ), Manjo-Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Buba ya bayyana cewa sojojin sun kuma kubutar da jimillar mutane 139 da aka yi garkuwa da su tare da kwato tarin makamai da alburusai da suka hada da muggan makamai 141 da alburusai iri-iri kimanin  1,463.

Wadannan ayyuka da ya ce an gudanar da su a fadin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma daga rundunonin soja daban-daban ne.

Buba ya ce, sojojin sun kuma kwato kayayyakin yaki daga hannun ‘yan ta’addan da suka hada da GPMG daya, bindiga kirar GT3 daya, bindigogi kirar AK47 guda 49, bindigar Josef Magnum Pump Action guda daya, bindigar ganga biyu.

Sauran sun hada da: bindigogi tara na gida, gurneti 13, bindigogin gida guda bakwai, da kuma gurneti na gida guda biyu.

A yankin Arewa maso Gabas, ya ce dakarun Operation Hadin Kai a watan nan na Nuwamba, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hada baki da ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa wasu ‘yan ta’adda ne suka tilasta musu yin tafiya tare da su don zame musu a matsayin masu kwarmata bayanan ayyukan sojoji.

Buba ya ce ‘yan ta’adda 108 da iyalansu da suka hada da maza 13, mata 32 da yara 63 ne suka mika wuya ga sojoji a tsakanin ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 23 ga watan Nuwamba a shalkwatar Rundunar OPHK.

Kazalika, ya ce sojojin sun kashe ’yan ta’adda 19, sun kama 21 tare da kubutar da wasu mutane takwas da aka yi garkuwa da su a cikin makon da ya wuce kamar yadda aka ambata.

A yankin Arewa ta tsakiya, Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven sun kashe ‘yan ta’adda uku, sun kama 32 tare da kubutar da mutane takwas da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai da alburusai iri-iri da dai sauransu.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja