Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ke shirin kai hari ga masu gyaran layin lantarkin Arewa

Jiragen yaƙin sojoji sun halaka ’yan ta’adda da ke shirin kai sabon hari kan masu aikin gyaran babban layin lantarkin Arewa da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna da ke ƙoƙarin gyarawa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ke shirin kai hari ga masu gyaran layin lantarkin Arewa

Jiragen yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya sun halaka ’yan ta’adda da ke shirin kai sabon hari kan babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna da ke ƙoƙarin gyarawa.

’Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu a hannun sojoji ne a ranar Juma’a, a yayin da ma’aikata ke ƙoƙarin gyara babban layin lantarkin da ke ɗauko lantarki daga Babbar Tashar Shiroro, ya raba wa yankin Arewa.

Kakakin rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce an halaka su a Dajin Alawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito yadda johohin Arewa 17 sun shafe kwanaki 10 babu wutar lantarki a sakamakon lalacewar layin lantarkin, bayan harinnda ’yan ta’adda suka kai masa.

Daga bisani Shugaba Tinubu ya umarci Minista da Manyan Hafsoshin Tsaro da Mashawarcinsa kan sha’anin tsaro su umarci dakarun su da su ba da cikakkiyar kariya ga ma’aikatan lantarki domin su gyara wutar.

Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce, “Da jiragen yaƙin suka yi arba da ’yan ta’addan suka bude musu wuta tare da ragargazar su da kayan aikinsu.”

Ya ci gaba da cewa jiragen sun mamaye sararin samaniyar yankin da ake gyaran domin hana ɓata-garin sakat wajen kawo cikas ga aikin gyaran.