Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 5 a Yobe

An kashe su ne a garin Gaidam na Jihar Yobe

Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 5 a Yobe

Wasu sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya da ke yaki da taaddanci sun samu nasarar kashe wasu mayakan da ake zargi yan kungiyar Boko Haram ne guda 5 a garin Gaidam na Jihar Yobe.

Sun ce sun sami nasarar ce yayin wata ba-ta-kashi da suka yi a daren Laraba.

Bayanan da Aminiya ta tattaro sun nuna cewa a cikin musayar wutar, dakarun sojan sun samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 da kuma babura na maharan.

Kazalika, ranar da lamarin ya faru, sauran ’yan ta’addan sun gudu da harbin bindiga a jikinsu.

Wani dan kasuwa a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa mazauna yankin sun ji dadin lamarin, inda ya ce ayyukan ’yan Boko Haram a yankin ya karu a ’yan kwanakin nan.

“Mun yi farin ciki da martanin gaggawa da sojojin Najeriya suka yi a nan Geidam inda suka kashe ’yan Boko Haram biyar. Wannan ci gaban na zuwa ne a lokacin da manoma da dama ke fargabar zuwa gonakinsu sakamakon karuwar hare-haren da suke kaiwa.

“A cikin watanni biyun da suka gabata, sun kashe jami’an tsaro sama da 3 tare da yi wa manoma barazana, inda jama’a ke korafin cewa jami’an tsaro ba su yi komai ba don shawo kan matsalar don haka sojoji ba su ji dadin hakan ba, shi ya sa dakarun Operation Lafiya Dole suka yi kokarin rage hare-haren,” inji shi.

Aminiya ta rawaito yadda wasu da ake zargin ’yan tayar da kayar baya ne suka kai hari a gidan kwastam da ke garin Geidam, inda suka kashe wani jami’i mai suna Usman Gombe a ranar Asabar da ta gabata.

Wani shugaban al’umma a Geidam, Ambasada Khalid Geidam, ya ce sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne biyo bayan sahihan bayanai game da ayyukan Boko Haram a kewayen Jororo.

Haka nan wani mazaunin garin na Geidam da shi ma ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya shaida wa Aminiya ta waya cewar mazauna garin na cike da farin cikin kashe ’yan ta’addan.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi