Sojoji sun kuɓutar da jarirai 2 da mata 5 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Mutanen da aka sace a kauyen a Jihar Neja an ceto su ne a Jihar Zamfara.

Sojoji sun kuɓutar da jarirai 2 da mata 5 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Sojojin Najeriya

Rundunar Operation Hadarin Daji ta Sojin Kasa ta ceto jarirai biyu da mata biyar a dajin Kuyambana da ke Jihar Zamfara, wadanda aka sace a ƙauyen Marange da ke ƙaramar hukumar Kagara a Jihar Neja tun a watan Janairun 2024.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Hadarin Daji, Laftanar Suleiman Omale ya fitar ranar Juma’a.

Omale ya ce, an kuɓutar da waɗanda lamarin ya rutsa da su ne ta hanyar farmakin da sojojin suka kai a yankin Kuyambana na Jihar Zamfara.

“An yi nasarar ceto mutanen ne sakamakon matsin lamba da sojojin suka yi wa ‘yan bindigar, wanda hakan ya sa aka kuɓutar da waɗanda abin ya shafa daga sansanin ‘yan bindigar.

“Samamen da sojojin suka yi a ranar 13 ga Maris, 2024 ya zama silar samun ‘yanci ta wadanda aka yi garkuwar da su,” in ji shi.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna