Sojoji sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Benuwe

Hedkwatar hukumar tsaro ta ce, dakarunta  da aka tura shiyyar Arewa ta Tsakiya  don yakar ‘yan bindigar da suka addabi jama’ar yankunan sun yi nasarar kubutar da mutum uku da aka yi garkuwa  da su a wani gida na iyalan kasungumin dan bindigar nan da aka fi sani da Gana a unguwar Gbise da ke […]

Sojoji sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Benuwe

Hedkwatar hukumar tsaro ta ce, dakarunta  da aka tura shiyyar Arewa ta Tsakiya  don yakar ‘yan bindigar da suka addabi jama’ar yankunan sun yi nasarar kubutar da mutum uku da aka yi garkuwa  da su a wani gida na iyalan kasungumin dan bindigar nan da aka fi sani da Gana a unguwar Gbise da ke karamar hukumar Katsina Ala ta jihar Benuwe.

Kakakin hukumar tsaron Kanal Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan, inda ya ce rundunar sojojin ta kubutar da namiji daya da mata biyu a wani samame da sojojin suka kaiwa ‘yan bindigar a safiyar jiya Juma’a.